Published September 1, 2023 | Version v1
Journal article Open

Tarihi A Wa}e: Nazari Akan Wa}ar Shahara Ta Aminu Ladan Abubakar Alan Wa}a

Creators

Description

Wa}a zance ne mai tattare da hikima da tsari cikin sautin murya mai za}i da jan hankali wadda ake yin ta domin isar da wasu sa}onni da za su amfanar da jama’a. irin wannan sa}o shi ake kira da jigo wanda yake bijirowa ta fannoni daban-daban cikin sha’anoni da suka shafi rayuwar al’umma. Mawa}a kuwa wasu mutane ne da Allah (SWT) yah ore masu wata baiwa ta hikimar iya sarrafa zantuka da kalmomi a wa}o}i da nufin garga]i ko wa’azi dangane da wasu abubuwa marasa kyau da ake aikatawa, wa]anda ka iya gur~ata rayuwar Jama’a. Wani lokaci kuma mawa}an kan sarrafa zantuttuka ko kalmomi a wa}o}insu domin nisha]antarwa ko kwarzanta wasu mutane da suka yi fice a wasu fannoni da suka shafi rayuwa ta yau da kullum. Wannan yanayi na jujjuya kalma ko sarrafa zance a wa}a shi ake kira da salo, wanda yake nufin duk wata dabara ko hanya da aka bi yayin aiwatar da wa}a domin isar da wasu sa}onni. Irin wannan dabara ta kan yi wa wa}a kwalliya ta yadda sa}on dake }unshe a wa}ar zai samu isa koi tsaye ga masu saurare. Aminu Ladan Abubakar (ALA) yana daga cikin mawa}an Hausa na zamani wanda ya shahara a fagen rera wa}o}in Hausa da suka danganci fannonin rayuwa daban-daban, kama tun daga kan wa’azi, fa]akarwa, ilmantarwa, shugabanci da kuma wa]anda suka shafi harkokin siyasa. Ma}asudin wannan mu}ala shi ne tsokaci kan yadda mawa}in ya yi amfani da salon tarihi a wa}arsa ta shahara.

Files

New article 12.pdf

Files (309.8 kB)

Name Size Download all
md5:b51c1b241751311e59e68057b2f89be3
309.8 kB Preview Download