Published September 1, 2023 | Version v1
Journal article Open

Arulin Hausa:Bitar Illa A Cikin Wasu Baitocin Waqoqi

Description

Aruli wani fannin ilmi ne da ake amfani da shi domin nazarin waqa, musamman rubutacciya. Kamar kowane fanni na ilmi, shi ma aruli yana da qa’idoji da kalmomi na fannu waxanda suka kevanta da shi. Wannan takarda za ta yi qoqarin duba ne kan wasu baitoci na waqoqin Hausa da ake samun illa a cikinsu da kuma fito da bayanin nau’inta. Haka kuma za a waiwaiya game da ma’anar aruli da gava da qafafuwa da kuma karuruwan da aruli ya qunsa a taqaice. Sannan za a yi bayani dangane da yadda ake samun illa, ko sakiya kamar yadda waxansu masana suka kira ta. Duba da yadda take afkuwa a cikin waqa,ta hanyar kafa madoga da wasu daga cikin waqoqi. Kazalika, takardar za ta bibiyi nau’o’in illa da kuma nau’in naqasun da ke shiga a cikin kowace gava da ke cikin qafa.

Files

New article 6.pdf

Files (379.0 kB)

Name Size Download all
md5:4ea15ab811d44c32a7c1463e984b8b4f
379.0 kB Preview Download