Published 2025 | Version v1

Yarfe a Tarihin Siyasar Jam'iyyu a Ƙasar Hausa: Duba Cikin Rubutaccen Zube

  • 1. Amsoshi Language Services
  • 2. ROR icon Federal University Gusau

Description

Manufar wannan takarda ita ce nazartan yadda ‘yan siyasa suke amfani da abubuwa na ɓatanci ga abokan hamayyarsu na siyasa. Tunanin wannan takarda ya taso ne duba da yadda ‘yan siyasa suka mayar da wannan abu tamkar in babu shi to siyasar ma ba za ta yiwu ba. Wannan ya sa aka ga dacewar a shiga cikin ayyukan adabi na rubutaccen zube a gani shin ‘yarfe’ yana da asali ne tun kafuwar siyasar jam’iyyu ko kuwa bai daɗe da samuwa ba? An yi nazarin yarfe a cikin tarihin siyasa da aka kundace a cikin ayyukan rubutaccen zube. An ɗora binciken kan ra’in ‘Tarihanci’ inda ya yi jagorancin zaƙulo tarihin yarfe a harkokin siyasar ƙasar Hausa. Takardar ta gano cewa, yarfe abu ne da ya ginu a cikin siyasar jam’iyyu tun daga farkon lamari. Bugu da ƙari, har yanzu ana amfani da shi domin neman ƙarin mabiya da kuma shafa wa abokan hamayyar siyasa kashin kaji, wanda hakan kan taimaka ga samun nasara ko faɗuwa a zaɓe.

Files

Yarfe a Tarihin Siyasar Jam’iyyu a Ƙasar Hausa - Duba Cikin Rubutaccen Zube.pdf

Files (395.5 kB)