Nazari Kan Zaɓar Jarumai ('Yan Wasa) A Fina-finan Hausa
Description
Tsakure: Wannan maƙala nazari ne kan zaɓar jarumai ('yan wasa) a fina-finan Hausa, waɗanda su ne ƙashin baya a harkar gudanar da shirin fim. Domin gudunmawarsu a gabatar da saƙon fim tana da muhimmanci. Saboda daga gare su ne manufar fim take isa ga masu kallo. Bisa ga irin matsayin da suke tattare da shi ne ya sa za a gabatar da bayanai a kansu. Muhimmancin wannan aiki shi ne a binciko yadda ake zaƙulo jarumai a fagen shirya fim na Hausa. An yi amfani da hanyar lura da karance-karance da tattaunawa wajen tattaro bayanai da aka sarrafa. Sannan an yi amfani da Ra'in Nazarin Ƙwaƙƙwafi a aikin adabi (Close Reading) wanda Richards da Empson (1940) suka ƙirƙiro domin gudanar da binciken. Wannan ra'i wani nau'in gudanar da bincike ne ta hanyar karantar ayyukan adabi ko na harshe waɗanda suke a rubuce ko abin da ake amfani da shi wajen hanyar sadarwa. Binciken ya gano cewa ana amfani da matakai daban-daban wajen tantance jarumai kafin su fito a cikin kowane irin shiri na fina-finan Hausa.
Abstract
Abstract: This paper, audition in Hausa Films (selection of actors in Hausa films production), discusses how actors are selected for film production. Actors in films are the backbone of the transmission of messages in film production. Their contribution is immense as it is through their artistry that messages are sent to the audience. The importance of this work is to discuss how actors are selected in the production of Hausa films. Reading and discussion methods are used in collecting and analyzing the data. Close Reading theory adopted in conducting the research is formulated by Richards and Empson (1940). This research theory concentrates on reading and analyzing written works in literature and language or any other works on media and films. The research finds that different methods are used during the selection of actors before they are presented in any film production.
Files
Chapter 5_Gandu.pdf
Files
(903.7 kB)
| Name | Size | Download all |
|---|---|---|
|
md5:4d31b977c15d880235c22d6ff79f8aaf
|
903.7 kB | Preview Download |