Published September 1, 2023 | Version v1

Rubutacciyar Waqa A Matsayin Hanyar Bayyana Takaici: Misalai Daga Waqar Wasiqa Ta Auwalu Anwar

Authors/Creators

Description

Wannan aiki mai suna “Rubutacciyar Waqa a Matsayin Hanyar Bayyana Takaici: Misalai Daga Waqar Wasiqa ta Auwalu Anwar” ta gudana ne don ta fito da yadda fasihi yake amfani da aikinsa na fasaha don bayyana hoton abin da yake damunsa a zuciya ga jama’a. Don kyautatuwan aikin, sai aka yi amfani da ra’in katanta (expressive theory) wanda M.H. Abrams (1912-2015) ya qirqiro wadda take magana dangane da alaqar fasihi da aikinsa na fasaha tare da yadda zuciyarsa take taimaka masa wajen sarrafa abubuwan duniya wajen samar da aikinsa na fasaha. An yi amfani da hanyar lura (observation) a matsayin ginshiqiyar hanyar tara bayanai, tare da bibiyar wasu ayyukan da masana suka rubuta a matsayin ‘yan rakiya. Nazarin ya fahimci cewa fasihai sukan yi amfani da hanyar fasaha wajen yin hannunka mai sanda ga masu mulki tare da bayyana masu irin cututtukan da suka dabaibaye su, kana kuma su haska masu irin al’amarin da ka iya faruwa gare su a gaba matuqar ba su canja ba cikin hikima da fasaha. Haka kuma, takaici kan sa su zarce ga furta abin da bai kamata a furta ba da yake cikin zuciyarsu. Daga qarshe kuma aka raka da manazarta.

Files

New article 20.pdf

Files (867.7 kB)

Name Size
md5:a95d4d50fe969074e313e0af1a063e01
867.7 kB Preview Download